A watan Yunin 1934 aka dauki hoton nan na gwamnan arewacin Najeriya Lord Lugard da wasu sarakunan kasar a wani Gidan Zoo a Landan
Tarihi ya tabbatar da cewa bayan jihadin Shehu Usman Bn Fodio, masarautu a kasar Hausa musamman wadanda Shehu ya bai wa tuta suna karkashin shugabancin daular ce, wato ayyukansu da tsari na shugabancinsu kamar naɗa sarki ko cire shi yana tabbata ne tare da sahalewar Fadar Sarkin Musulmi da ke da hedikwatarta a Sakkwato.
Haka abun ya ci gaba har zuwan Turawan Mulkin Mallaka wadanda suka sauya wannan tsarin ya dawo karkashin ikonsu.
Ina so ne na jawo hankalin mai karatu ya fahimci yadda ƙarfin ikon masarautun yake raguwa har zuwa wannan lokaci da ake ganin ƙarfin masarautun ya faɗi warwas.
A zamanin da suke ƙarƙashin Daular Sarkin Musulmi, ana naɗa sarki ne a bisa cancanta da alaƙa ta asali da gadon sarautar.
Haka Turawa suka ci gaba da yi a lokacinsu, wato a duk lokacin da sarki ya mutu, masu zaben sarki za su tura wa gwamna waɗanda suka tantance a cikin masu neman sarautar, shi kuma zai zaɓi wanda ya ga ya fi dacewa ya amince da naɗinsa a matsayin sabon sarki.
Wannan tsari ya ci gaba da tafiya har bayan samun ƴancin kai da kuma zuwan mulkin soja a ƙasar nan.