Kasafin Kuɗin Najeriya na 2021: Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin naira tiriliyan 13.08

 Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kuɗin ƙasar kimanin naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021 a gaban Majalisar Dokokin ƙasar - a zaman hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai.

Hasashen kuɗin ya fi na bara da tiriliyan 2.28, inda na baran ya kasance naira tiriliyan 10.805.

A yayin da yake gabatar da kuɗin Shugaba Buhari ya ce samun kuɗaɗen shiga don amfani da su wajen kasafin kuɗin shi ne babbar matsalar da gwamnatinsa ke cin karo da shi.

Sannan kuma ya ce ministoci za su dinga sa ido don tabatar da cewa hukumomin karɓar kuɗaɗen haraji na ayyukansu yadda ya kamata.

Shugaba Buhari ya bayyana ƙudurin kasafin kuɗin da cewa na farfaɗo da tattalin arzikin kasa ne, bisa la'akari da ƙalubalen da Najeriya, kamar sauran kasashen duniya ta fuskanta daga annobar korona, wadda ta durƙusar da tattalin arziki ta ɓangarorin rayuwa daban-daban.

Kuma wannan ya sa gwamnati ta zurfafa tunani wajen tsara hanyoyin raya tattalin arzikin da kasafin kuɗin da ake sa ran zai ci mukuɗan kudaɗe.


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post