Wace ce wannan mata da ke son kawo sauyi a Najeriya?


 Matakin da rundunar 'yan sandan Najeriya ta dauka na rusa sashenta da ke yaki da fashin da makami, wanda aka fi sani da SARS a takaice, ya sanya 'yan kasar murna matuka.

Gabanin wannan mataki, 'yan Najeriya sun kwashe shekara da shekaru suna fafutukar ganin an rusa rundunar SARS, wadda ake zargi da cin zarafi da azabtarwa da ma kashe mutanen da ta kama.

Sai dai wani muhimmin abu da ya fito fili tun bayan rusa SARS shi ne irin rawar da masu fafutuka suke takawa wurin kawo sauyi a duniya.

Aisha Yesufu na cikin mutanen da suka kwashe shekara da shekaru suna fafutukar ganin an samar da mulki na gari a Najeriya, kuma sunanta ya kara fitowa fili a lokacin da ta shige gaba wajen fafutukar ganin an ceto 'yan matan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a 2014.

A wannan karon ma, ta taka muhimmiyar rawa a zanga-zangar kyamar SARS inda wani hotonta da ta bijirewa 'yan sanda ya karade shafukan intanet na kasar.

Wani abu da ya bambanta ta wajen wannan fafutuka shi ne yadda ake saukin gane ta saboda ko da yaushe tana sanye da hijabi.


1 Comments

Post a Comment
Previous Post Next Post