Yayin cinikayyar bayi zuwa tsallaken tekun Atalantika, miliyoyin 'yan Afirka ne aka tilasta musu shiga ƙangin bauta.
Akwai labarai da yawa kan muni da ƙazancewar lamarin bautar, har ma da wasu abubuwa na zahiri da suka yi saura game da ita.
A wani kogi da ake kira Donkor Nsou, wato Kogin bauta. a nan ne bayin da suka yi tafiyar sama da mil ɗari uku cikin mari da sarƙa daga arewacin Ghana sukan yi wankan ƙarshe.
Daga nan sai su wuce zuwa gaɓar kogin inda a kan shafa musu mai don jikinsu ya yi kyau.
Filin ya kai murabba'in mita 70 faɗinsa, da tsawon mita 80, ana ganin nan ne kasuwar bayi mafi girma a Gold Coast ƙasar Ghana a yanzu.