Wasiƙa daga Afrika: Me ya sa ake barazana ga 'yan jarida a Najeriya?

 Tsohon minista Femi Fani-Kayode ya yi ta cin mutuncin ɗan jaridar kamar wanda aka yi wa baki

Cikin jerin wasiƙun da muke samu daga 'ƴan jarida daga Afirka, tsohon babban editan jaridar Daily Trust, Mannir Dan Ali ya duba ƙalubalen da 'ƴan jarida ke fuskanta a yayin gudanar da ayyukansu.

A Najeriya har yanzu ana tambayar ko me ya sa jami'an gwamnati suke yi wa 'ƴan jarida kallon yaransu.

Wannan ya biyo bayan ƙurar da ta tashi sakamakon cin mutuncin da tsohon minista a Najeriya, Femi Fani Kayode kuma ɗan jam'iyyar adawa ta PDP ya yi wa wani ɗan jarida.

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda Femi Fani-Kayode ya fusata saboda wata tambayar da ɗan jarida, Eyo Charles ya yi masa yayin wata hira da 'yan jarida.


Post a Comment (0)
Previous Post Next Post