Rabi'u Kwankwaso: Gwamnatin Buhari ba ta damu da halin da 'yan Najeriya ke ciki ba


 Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a babbar jam'iyar hamayya ta PDP Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga gwamnatin kasar ta janye matakan da ta dauka a baya-bayan nan na kara farashin man fetur da kuma na wutar lantarki, da ya ce za su kara jefa jama'a cikin mawuyacin hali.

Kwankwaso ya ce kamata ya yi gwamnatin ta toshe hanyoyin da kudade ke zurarewa a maimakon karin farashi.

Tsohon gwamnan wanda yanzu haka ke ziyarar karfafa gwiwar magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar Edo gabanin zaben gwamnan jihar da za a yi a makon gobe, ya shaida wa BBC cewa babu hujjar karin farashin a wannan lokaci.

Ya ce "Kasashe da yawa a duniya a yanzu shugabanninsu na tausaya musu inda suke fito musu da tsare-tsare ta yadda zasu samu saukin radadin wannan annoba ta korona, amma sai gashi a Najeriya a irin wannan yanayi aka shigo da duka na karin farashin mai da wutar lantarki da dai sauran abubuwa'.

''A gaskiya da wuya ka samu wani wanda zai goyi bayan wannan tsari'' in ji shi.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post